Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: A matsayin ci gaba da aikin ramuwa na daren jiya, jaruman mayaƙan na rundunar sararin samaniya ta Rundunar Tsaron Juyin Juya Hali, a karo 15 na aikin Nasr 2 tare da lambar sirri ta "Ya Abasalihil Mahdi Adrikni" sun kai wani hari mai tsanani da ban mamaki a sansanin sojan sama na Amurka a Al-Udeid na Qatar, inda suka lalatar da na'urar radar mai dogon zango gaba daya da jiragen sama masu yawa da ke daukar man fetur don karawa jiragen yakin Amurka, tare da yin mummunar barna ga wasu jiragen.
Wannan aikin da nasararsa sadaukarwa ne ga shahidan da Amurka ta kaiwa hari baya-bayan nan, domin hukunta masu cin zarafi da kuma azabtar da sojojin Amurka masu kashe yara,
Abokiyar gaba Amurka da masu masaukin sansanoninta a yankin su sani cewa ƙetare jajayen layukan da kai hari kan mutane da ababen more rayuwa na farar hula zai haifar da azabrta garesu mai tsanani da talauci, kuma idan makiya suka ci gaba da wannan yanayin, akwai martani masu ruguzawarwa da rubdarwa a kan hanya; martani da za su dawwama a tarihin yaƙe-yaƙe.
Ku Yake Su Har Sai Ya Kai Ga Babu Wata Fitina Da Kuma Addini Ya Kasance Ga Allah Shi Kadai
"Kuma Babu Wata Nasara Fa Ce Daga Allah Mabuwayi Mai Hikima".
Ra'ayinka